• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN YANKEWA WADUME DAURIN SHEKARU 7 A GIDAN YARI

Alkalin babbar kotun taraiyar Najeriya a Abuja Binta Nyako ta yankewa wanda a ka kama da laifin satar mutane Bala Wadume daurin shekaru 7 a gidan yari.

Labarin hukuncin da a ka yanke tun 22 ga watan jiya bai fito ba sai a farkon makwan nan.

Wadume dai wanda a ka kamo daga jihar Taraba inda ya yi wuf ya arce daga hannun ‘yan sanda amma a ka cafke shi a Kano, ya ce wasau abububwan da a ke zargin sa da su kamar satar mutane bait aba sace kowa ba.

Kotun ta yanke hukuncin kan caji na 2 da na 10 cikin 13 da a ke tuhumar sa da su ka shafi arcewa daga hannun ‘yan sanda da kuma mallakar makamai ba bisa ka’idar doka ba.

Da alamu tuni Wadume ya share 3 daga cikin wa’adin shekarun da zai share a gidan yari inda zuwa wani lokaci ma zai kammala dukkan wa’adin an duba yanayin shekarar dauri daban ce da shekarar kalanda.

Ba shakka girman labarin cafke wadume kan tuhumar satar mutane zai zama na biyu ne kawai in an ambaci da gagarumin barawon nan Evans da a ka yankewa hukuncin daurin rai da rai

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.