• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN TURA FAROUK LAWAN GIDAN YARIN KUJE

ByYusuf Yau

Jun 24, 2021 ,

Biyo bayan hukuncin daurin shekaru 7 da babbar kotun Abuja ta yankewa tsohon dan majalisa Farouk Lawan, yanzu an tura shi gidan yarin Kuje.

Shi dai wannan gidan yarin shi ne na Abuja da ke garin Kuje daf da filin saukar jiragen sama na Abuja.

Alkalin babbar kotun ta Abuja Angela Otaluka ba ta amince da hujjar da Lawan ya bayar ba amma ta gamsu da hujjar Femi Otedola da ya mika kudin rashawa dala dari 500.

In za a tuna Farouk Lawan ya jagoranci kwamitin binciken wadanda su ka yi sama da fadi da kudin tallafin fetur a 2012 da hakan ya sa ya shiga zargin neman rashawar fidda kamfanin Otedola da ya amshe dala miliyan 230 daga kamfanin fetur NNPC don shigo da fetur amma hakan bai yiwu ba.

Lawan ya yi kokarin shaidawa kotu ya amshi dala dubu 500 don zama hujjar kama Otedola da laifi yayin da shi ma Otedola ya ce ya ba wa Lawan kudin ne don kama shi da laifi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *