• Fri. Dec 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari...

AN TSIGE MATAIMAKIN GWAMNAN JIHAR ZAMFARA MAHADI ALIYU

Majalisar dookokin jihar Zamfara ta tsige mataimakin gwamnan jihar Mahadi Aliyu bayan kwamitin bincike ya mika ma ta sakamakon zaman da a gudanar.
Majalisar ta dau matakin ne jim kadan bayan kwamitin binciken da babbar alkalin jihar Kulu Aliyu ta jagoranta.
An ruwaito kakakin majalisar Nasiru Magarya na cewa kwamitin binciken ya samu Mahadi da laifin da a ke zargin sa da aikatawa.
Membobin majalisar 20 da su ke nan lokacin da a ka kawo batun tsigewar sun amince da matsayar da kawar da Mahadi daga kujerar.
Gabanin nan mataimakin gwamnan ya dau matakin kin baiyana gaban kwamitin inda ya ce ya nufi kotu kan batun tsige shi.
Mahadi Ali dai ya samu sabani da gwamnan Zamfara Bello Matawalle bayan kin sauya sheka tare da shi zuwa APC.
Ba wannan shi ne karo na farko a dimokradiyyar Najeriya da a ke samun tsige mataimakin gwamna ba, biyo bayan sauya shekar gwamna.
In za a tuna a lokacin da tsohon gwamnan Bauchi Isa Yuguda ya sauya sheka daga ANPP zuwa PDP, marigayi mataimakin sa Garba Gadi ya zauna a ANPP, inda daga nan majalisar jihar ta tsige shi.

Duk da dawo da shi da kotu ta yi, bai sa Gadi ya samu nasarar gudanar da aiki ba, inda yak an fito ofis ya zauna amma ba a turo ma sa wani abu da zai aiwatar.

KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
59 thoughts on “AN TSIGE MATAIMAKIN GWAMNAN JIHAR ZAMFARA MAHADI ALIYU”
  1. Fantastic goods from you, man. I have take note your stuff prior to and you are simply extremely wonderful. I actually like what you’ve bought right here, certainly like what you’re stating and the best way in which you assert it. You are making it enjoyable and you still care for to stay it sensible. I can’t wait to learn far more from you. That is actually a wonderful site.

  2. An interesting dialogue is worth comment. I think that it is best to write extra on this subject, it won’t be a taboo topic but typically individuals are not sufficient to talk on such topics. To the next. Cheers

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *