• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN TONO GAWAR INIOBONG-MATAR DA TA BACE A YAYIN NEMAN AIKI A AKWA IBOM

Karshe an gano cewa wata mata mai suna Iniobong Umuoren da ta bace a tafiya zantawar neman aiki a jihar Akwa Ibom kashe ta a ka yi a ka bunne ta a wani karamin kabari.

Iniobong wacce ta kammala karatu a jami’ar Uyo ta fita neman aiki ne a wajen babban birnin jihar Uyo inda matashin da ya yi ma ta alkawarin aikin mai suna Uduak Akpan ya yaudare ta zuwa gidan mahaifin sa inda ya yi ma ta fyade daga nan ya kashe ta kuma ya bunne ta a harabar gidan.

Uduak Akpan mai shekaru 20 ya saba yi wa mata fyade a baya ta hanyar irin wannan yaudara.

An cafke Akpan kuma za a gurfanar da shi gaban kotu don amsa laifukan fyade da kashe rai ba da hakkin shari’a ba.

Rundunar ‘yan sanda a jihar ta yabawa ma’abota yanar gizo don yanda su ka yayata kamfen na neman inda Umuoren ta shiga bayan an rasa inda ta ke yayin da ta fita neman aiki.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *