• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN TILASTA MAHAIFI NA YA BA WA BEBRAN BASSIL HAKURI – MASRI

Matar nan ‘yar Lebanon da ta sha yabo don tozarta dan majalisar dokokin kasar Gebran Bassil da ta yi, ta ce an tilasta mahiafin ta ya ba wa Bassil din hakuri amma sam ba ta ja da baya ba.

Matar mai suna Yasmine Masri ta na wani dakin abinci be da kawayen ta, yayin da ta ga Bassil da tawagar sa ta jami’an tsaro inda ta yi ma sa ele da ihun cewa yaji kunya.

Nan dai jami’an tsaron Bassil su ka lalata wayar salular Yasime inda daga bisani a ka yada hoton Bassil da mahaifin Yasmine da nuna an ba shi hakuri.

Bassil dai surukin shugaban Lebanon Michel Aoun ne da a ke dauke ya na kan gaba a ‘yan jari hujjan da su ka talauta Lebanon.

Mutane sun yi murna da yanda Yasmine ta zubarwa Bassil kima da caccakar sa ido da ido ba tare da fargaba ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *