Hukumar jiragen kasa ta takaita da zirga-zirga tsakanin Abuja da Kaduna don harin da miyagun iris u ka kai kan titin jirgin a wajajen yankin Rijana da ke zama tungar barayin daji.
Rahoton ya baiyana cewa barayin sun dasa nakiyoyi kan titin jirgin da hakan ya jawo gocewar digar jirgin.
Hakanan barayin sun bude wuta kan jirgin da nufin dakatar da tafiyar sa amma Allah ya kiyaye ba su cimma burin su ba.
An ga faya-fayan bidiyo a yanar gizo na inda a ka dasa nakiyoyin da fasinjoji su ka dauka.
Kafin aukuwar akasin, fasinjoji sun fi samun natsuwa su shiga jirgin kasa maimakon bin titin mota don gudun gamuwa da barayin.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
Why users still use to read news papers when in this technological world the whole thing is available on web?