• Wed. Jun 29th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN TAFKA RUWAN SAMA KAMAR DA BAKIN KWARYA A BIRNIN RIYADH NA SAUDIYYA

An tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya da iska a babban birnin kasar Saudiyya wato Riyadh inda hakan ya tilasta dakatar da hada-hada ta waje da rufaffun sassa.
An dakatar da taruka da yawa da a ka shirya a birnin duk da mahalarta tarukan yawanci na nishadi na sanye da rigunan ruwa kuma rike da lema.
A na sa ran gudanar da tarukan a asabar din nan in ruwan ya tsagaita.
Baya ga Riyadh, hukumar kula da yanayi ta Saudiyya ta ce za a samu ruwan a birnin Makkah, Madina, Hail, Qassim da yankin Alkhobar.
Hukumar yanayin ta yi gargadin za a iya samun ambaliyar ruwa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
3 thoughts on “AN TAFKA RUWAN SAMA KAMAR DA BAKIN KWARYA A BIRNIN RIYADH NA SAUDIYYA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.