• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN SHIGA KUSAN JAJIBERIN ZABEN FIDDA GWANI NA JAM’IYYU, ‘YAN TAKARA SUN TAKARKARE

Yayin da za a ce an shiga kusan jajiberin zaben fidda gwani na jam’iyyu a Najeriya, ‘yan takara na kara takarkrewa don jan hankalin wakilan da za su kada kuri’a.

Allunan tallar ‘yan takarar sun karade manyan biranen Najeriya musamman Abuja.

APC da PDP za su gudanar da manyan tarukan fidda gwanin a Abuja da bambancin kwana daya a tsakani kuma da samun mafi yawan ‘yan takara.

Masana siyasa na nuna fargabar duk kuskuren da daya daga manyan jam’iyyun ta yi zai yi tasiri wajen tagomashin lashe zaben ta a 2023.

Tuni ma alamu na nuna magoya bayan manyan ‘yan takara zai yi wuya su rungumi kaddara, in an duba yanda ya faru a zaben fidda gwani na gwamnoni da ‘yan majalisa.

Tuni a wasu jihohi a ka samu baraka don rashin jin dadin yanda sakamakon zaben ya fito.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.