• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN SHIGA JUYAYIN RASUWAR JIKAN SARDAUNAN SOKOTO, HASSAN DANBABA

Al’ummar arewacin Najeriya sun shiga juyayin rasuwar jikan Sardunan Sokoto Sir Ahmadu Bello, Alhaji Hassan Danbaba.
Marigayin wanda shi ne magajin garin Sokoto ya rasu ne a gidan sa a Kaduna ya na mai shekaru 50.
Hassan Danbaba wanda ke da dabi’ar haba-haba da jama’a, ya samu shaidar taimakon jama’a da son cudanya da lamuran addini.
Duk labarun na nuna Allah ya yi wa marigayin rasuwa bayan fama da ‘yar gajeruwar jinya.
Magajin Gari ya rasu kimanin shekara daya bayan rasuwar mahaifiyar sa wacce ‘yar Sardunan Sokoto ce.
A shekarun baya a kan ga Hassan Danbaba a Saudiyya ya na taimakawa mahaifiyar sa wajen gudanar da aikin hajji ta hanyar tura ta a kan keken wadanda ke da lalurar tsufa ko ta takawa da kafa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.