• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN SHIGA JUYAYIN KISAN GILLA GA KWAMISHINAN KIMIYYA DA FASAHA NA KATSINA RABE NASIR

ByNoblen

Dec 10, 2021 ,

An shiga matukar juyayi bisa kisan gilla da wasu ko wani ya yi wa kwamishinan kimiyya da fasaha na jihar Katsina Malam Rabe Nasir a gidan sa da ke Katsina.
Labarin ya nuna an yi kisan gillar ne ta hanyar amfani da wuka a ka soki marigayin da kuma jan gawar sa a ka kulle ta a bayan gida.
Rabe Nasir wanda shaharerren ne don ya yi aiki a hukumae EFCC da zama dan majalisar wakilai, na sharhi kan lamuran inganta tsaro a Najeriya.
Tuni gwamnan Katsina Aminu Masari ya garzaya gidan marigayin inda a ka fito da gawar a ka kai asibiti inda a ka cigaba da gudanar da binciken abun juyayin.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Sunusi Buba ya ce an kama wani mutum daya da alaka da kisan.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *