• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN SAMU TARIN MAKAMAI A GIDAN DAN RAJIN KASAR YARBAWA SUNDAY IGBOHO

Rubdunar ‘yan sandan farin kaya ta Najeriya DSS ta ce ta gano makamai da dama a gidan dan rajin kafa kasar Yarbawa Sunday Igboho a Ibadan jihar Oyo.

A sanyin safiyar alhamis jami’an tsaron na DSS su ka samame gidan Igboho wanda a lokacin ya ke shirya gudanar da wani gangamin ‘yan arewa a Lagos.

Jami’in labarun DSS Peter Afunaya ya baiyana cewa an samu bindigogi kirar AK 47 guda 7, da na harbi ka ruga da ma albarusai dubu 5.

Afunaya ya ce an samu shiga gidan Igbaho ne bayan musayar wuta tsakanin jami’an da ‘yan gadin gidan.

A musayar wutar an kashe jami’an gadin gidan biyu inda kuma a ka ji wa daya rauni a hannu amma an kai shi asibiti.

Wasu kungiyoyin Yarbawa na nuna matakin take ‘yancin Igbaho ne.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *