• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN SAMU SULHU DA YARIMA HAMZA-SARKI ABDULLAH

ByNoblen

Apr 8, 2021

Sarki Abdullah na Jodan ya ce an sulhunta dambarwar tada fitina a Jodan don Yarima Hamza da a ka zarga da tada fitinar ya nuna mubaya’a ga sarki Abdullah da sauran zuriyar Hashimawa.

Sarki Abdullah ya ce Yarima Hamza na fadar sa tare da iyalin sa kuma karkashin kulawar sa, kazalika ya ce zai kare muradun gidan sarauta da bin hanyar iyaye da kakanni.

Yarima Hamza ya rubuta takardar mara baya ga sarki Abdullah.

Tuni shugaban Amurka Joe Biden ya bugowa sarki Abdullah waya ya na nuna goyon bayan sa ga Jodan.

Wannan takaddama ba ta rasa nasaba da fitinar gidan sarauta da ta samo asali tun lokacin da marigayi sarki Hussein ya sauya dan uwan sa a matsayin yarima mai jiran gado ya nada dan sa saki na yanzu Abdullah bin Hussein.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *