Sabuwar fitina ta barke a kasar Sham da ta shiga yakin basasa na tsawon shekaru 5 inda mafi munin hari a bayan-bayan nan, a ka dana bom a motar safa ta soja a birnin Damaskas inda mutum 14 su ka rasa ran su.
Boma-baman guda biyu sun fashe a cikin safa din a tsakiyar birnin Damaskas.
An ga jami’an agajin gaggawa na lekawa don tsamo sassan marigaya a wajen da boma-boman su ka sa motar ta tarwatse.
Akasin ya auku a dab da gadar Hafez Al’Asad kuma kusa da gidan ajiye kayan tarihi na Damaskas.
Wannan shi ne mafi munin hari a Damaskas tun 2017 inda ‘yan Daesh su ka kai farmaki kan cibiyar shari’a da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutum 30.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀