• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN SAMU RUDANI A HELKWATAR APC

An samu rudani a helkwatar APC mai mulki a Abuja yayin da labarin kwabe shugaban kwamitin rikwan jam’iyyar Mai Mala Buni ya fito a kafafen labaru.
Labarin dai ya nuna daga shugaba Buhari ne wanda ya ba da umurnin kwabe Mai Mala Buni, amma nan take jami’an jam’iyyar su ka ce labarin ba gaskiya ba ne.
Duk da baiyanar gwamnan Neja Abubakar Sani Bello a helkwatar jam’iyyar bai hana labaru masu cin karo da juna ba, da jami’an jam’iyyar ke cewa gwamnonin da su ka taru duk na goyon bayan Mai Mala Buni kuma ‘yar hatsaniyar ta shafi zaben shiyyoyi na jam’iyyar.
Babban jami’ain labarum jam’iyyar Salisu Na Inna Dambatta ya ce Mai Mala na kan kujerar sa.
Na tambayi gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje kan labarin inda ya ce a waje na ya samu labarin.
Koma dai me ya faru, Sanata Kabiru Gaya ya ce Mai Mala ya yi bakin kokarin rikwan jam’iyyar.
A yanzu haka Mai Mala Buni ya na ketare don haka za a jira karin bayanai a yayin da jam’iyyar ta sa aiyana 26 ga watan nan a matsayin ranar babbar taro.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
4 thoughts on “AN SAMU RUDANI A HELKWATAR APC”
  1. My brother suggested I might like this website. He was once totally right.

    This publish actually made my day. You cann’t believe just how so much time I had spent for this information! Thanks!

  2. After I initially commented I clicked the -Notify me when new comments are added- checkbox and now every time a comment is added I get four emails with the identical comment. Is there any manner you possibly can take away me from that service? Thanks!

Leave a Reply

Your email address will not be published.