• Wed. Dec 1st, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN SAMU RABUWAR KAWUNA A ZABEN APC A JIHOHI DA DAMA

ByYusuf Yau

Oct 17, 2021

AN SAMU RABUWAR KAWUNA A ZABEN APC A JIHOHI DA DAM

Rahotanni daga jihohi da daman a nuna an samu rabuwar kawuna a zaben shugabancin jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Yayin da a wasu daga jihohin a ka yi zabe guda biyu da samun shugabanni biyu musamman a Kano, wasu an tashi dutse hannun riga inda ya nuna su ma za su iya samun bangare.

A Kano gwamna  Abdullahi Umar Ganduje ya yi gargadin duk wani taro da ya saba da wanda ya ke ciki ya saba doka, amma hakan bai hana bangaren tsohon gwamna Sanata Ibrahim Shekarau gudanar da zaben bangare da ya fito da Ahmadu Haruna Danzago a matsayin shugaba.

Sanata Ibrahim Shekarau, Sanata Barau JIbrin da wasu ‘yan majalisar taraiya irin su Sha’aban Sharada na cewa ba za su lamunci yanayin jagorancin jam’iyyar karkashin Abdullahi Abbas ba.

‘Yan APC a Bauchi sun rabu gida biyu tsakanin masu mara baya ga ministan ilimi Adamu Adamu da kuma bangaren wadanda ke cewa an yi zalunci irin su Usman Tugga, Aliyu Gebi, Hassan Sharif da sauran su.

Duk da haka a jihar Gombe an samu nasarar zabe daya inda Nitte Amangal ya zarce kan kujerar.

Hakan ya nuna APC na da jan aikin sulhunta ‘ya’yan ta da ke arangamar siyasa da juna.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “AN SAMU RABUWAR KAWUNA A ZABEN APC A JIHOHI DA DAMA”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *