• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN SAMU KARIN KAMUWA DA CUTAR KYANDAR BIRI 10 A NAJERIYA A MAKO DAYA DA YA WUCE

An samu karin bullar cutar kyandar biri 10 a Najeriya a mako daya da ya wuce inda hakan ya nuna cutar na nan na yaduwa.

Cibiyar yaki da cutuka ta kasa NCDC ta baiyana wannan labarin da ya ke zaburar da jami’an kiwon lafiya wajen yaki da kwayar cutar.

Kyandar biri da ke haddasa kuraje su mamaye jikin mutum na kama da cutar agana da kan sa a ware mai fama da ita daga cikin sauran jama’a.

A halin yanzu a cikin duniya an samu bullar cutar 1000 a cikin kasashe 30 da su ka hada da turai da Amurka.

Hukumar lafiya ta duniya ta kwaranye fargabar zaman cutar annobar duniya kuma tuni wasu kasashe ke amfani da rigakafin agana don magance cutar kasancewar sun yi kama.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.