• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN SAMU KARANCIN RUWAN SHA A ABUJA BABBAN BIRNIN NAJERIYA

ByNoblen

Mar 26, 2021 ,

A yanzu haka a na fama da karancin ruwan famfo a babban birnin Najeriya Abuja da hakan ya haddasa mutane daukar jarka su na neman ruwan daga makwabta masu rijiyar burtsatse.

Birnin dai da ke aiki da ruwa a duk lamuran rayuwa, kan zama cikin damuwa da zarar famfo ya dauke ko da na tsawon wuni daya ne.

Rahoton da a ke samu na nuna ruwan ya samu natsala ne daga fashewar babban bututun da ke shigo da ruwa birnin daga madatsar ruwa ta Usuma a yankin Bwari.

Asalin tsakiyar garin mai tarin ‘yan jari hujja ba shi da masu tura ruwa a kura don haka a kan dogara ga masu rijiyar burtsatse don samun ruwan da za a yi amfani da shi ta wanki, wanka da bahaya.

Matsalar ta fi yawa a anguwannin da ke kan tudu inda in karfin ruwan ya yi kasa to ba zai haura ba, amma anguwannin gangare kan amfana da ruwan duk rashin karfin da ya ke da shi a bututu.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *