• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN SAMU GIDAJEN MAI A ABUJA DA KE SAYAR DA LITA FIYE DA NAIRA 165

ByNoblen

Jul 13, 2022

An gano gidajen mai da ke sayar da litar man fetur fiye da ka’idar gwamnati a cikin birnin Abuja.
An fahimci cewa gwamnati kan ba da tallafin fetur a man dava ke saukewa a gidajen man Abuja da hakan ya sa litar ta ke nan yanda a ka saba.
In ka fita daga Abuja gidajen mai na sayar da man bisa yanda za su samu riba kuma gwamnati ba ta zuba ido don ba ta ba da tallafi.
A Keffi jihar Nasarawa a kan sayar da litar fetur naira 185,
A Jos jihar Filato a kan samu litar man kan naira 190.
Akwai jihohin da kan sayar da man sama da naira 200.
Duk alwashin kamfanin mai NNPC na samar da man a Abuja amma matsalar dogayen layuka sai kara ta’azzara ta ke yi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
53 thoughts on “AN SAMU GIDAJEN MAI A ABUJA DA KE SAYAR DA LITA FIYE DA NAIRA 165”

Leave a Reply

Your email address will not be published.