• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN SAMU BARKEWAR ANNOBA KORONA A KASAR YAMAN

Annobar cutar korona ta barke a yankin Habaramout na shiyyar kudu maso gabashin kasar Yaman.

Hukumar lafiya ta duniya ta baiyana cewa daga watan Janairu na bana zuwa Agusta, a kasar ta Yaman an samu mutum 167,278 da su ka kamu da korona inda mutum 48 su ka rasa ran su.

Yankin Hodeida ya fi samun kaso mai yawa na mutum 26,936 sai babban birnin kasar Sanaa da mutum 24,593.

Jami’an lafiya na Yaman sun ce daga watan Afrilu zuwa yanzu an samu kimanin mutum 250 sun kamu da korona a yankin Hajjar.
A na cigaba da daukar matakan shawo kan annobar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.