An sallami Sarki Salman daga gadon asibitin Sarki Faisal a Jiddah bayan yi ma sa aiki da ya shafi babban hanjin sa.
Sarkin dai ya kwanta a asibitin tun makwan jiya inda likitoci su ka ba da shawarar ya zauna don kara hutawa da samun kulawa.
Gabanin kwanciya a asibitin Sarki Salman ya zauna a Makkah a fadar Sarki ta Alsafa da ke jikin haramin Masjidul Haram inda ya kammala azumi da gudanar da idin karamar sallah.
A can Daular Larabawa kuma da a ke zaman makokin mutuwar shugaban kasar Khalifa bin Zayed Al-Nahyan, shugaban Faransa Emmanuek Macron ya sauka a kasar inda ya gana da sabon shugaban kasar Muhammad bin Zayed Al-Nahyan.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀