Biyo bayan sako dalibai 27 na kolejin aikin noma ta Afaka da ke Kaduna daga hannun barayin mutane, yanzu saura na jami’ar Greenfield su 16.
An sako daliban na Afaka ne bayan share fiye da wata daya a hannun jagoran barayin mutane na gefen yammacin titin Abuja zuwa Kaduna mai suna BODERI.
Majiya mai inganci ta nuna Boderi da kan sa ya zo ya mika daliban bayan ya karbi fansar Naira miliyan 15 da kuma sako ma sa daya daga mutanen sa da a ka kama.
Faruwar wannan ya sa hankali ya koma kan sako daliban jami’ar Greenfield su 16 daga inda a ke tsare su cikin barazanar hallaka su matukar ba a turo Naira miliyan 100 ba.
Tuni barayin su ka kashe daliban jami’ar 5 da sako daya daga daliban bayan biyan diyyar Naira miliyan 20.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
I wanted to thank you for this great read!! I certainly enjoyed every little bit of it.
I’ve got you bookmarked to check out new things you post…
I do not even know how I stopped up right here, but I assumed this post used to be great.
I do not know who you are however certainly you’re going to a well-known blogger if you
are not already. Cheers!