• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN SAKI AMARYAR DA TA KIRBAWA MIJIN TA WUKA TA KASHE A 2014 A KANO

Kwamitin kula da rage cunkuso a gidajen yari na Najeriya karkashin Jostis Ishaq Bello ya sake amraya Rahma Hussein wacce ta kirbawa mijin ta wuka a 2014 ta kashe shi har lahira mako daya bayan auren su.

Tun farko kotu ta yanke hukuncin a daure Rahma bisa amincewar gwamnan Kano Abdullahu Umar Ganduje.

Rahma ta aika laifin lokacin ta na mai shekaru 16 don haka bisa dokokin Najeriya ba ta isa a yanke ma ta hukunci ba sai gyaran hali.

Kazalika an ba da shaidar cewa an yi wa Rahma auren dole ne.

Hakanan an ba da shaidar ta gyara halin ta a gidan yari.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.