• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN SAKE TSINTAR GAWAR DALIBAI BIYU NA JAMI’AR GREENFIELD

Gwamnatin Kaduna ta baiyana samun karin gawar daliban jami’ar Greenfield guda biyu biyo bayan sace su da ‘yan bindiga su ka yi.

Wannan ya zo ne kwana uku bayan samun gawar dalibai uku na jami’ar cikin adadin dalibai goma sha da a ka sace da nuna neman diyyar Naira miliyan 800.

Ba mamaki wannan wata hanya ce ta nuna tsanantar rashin imanin masu satar mutanen da ko ba a ba su kudin fansa ba, za su zubar da jinin wadanda su ka sace.

Gwamnatin jihar Kaduna da ta dau matsayar ba da kudin fansa, ta mika sakon ta’aziyya ga jami’ar bisa wannan rashi.

A sanarwa daga kwamitin harkokin cikin gida da tsaro na jihar Samuel Aruwan, ya ce an kai gawar daliban biyu dakin hutu.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *