• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN SACE TSOHON DARAKTAN NBC NA SHIYYAR BORNO AHMED ABDULKADIR

Barayin mutane sun sace tsohon daraktan hukumar kula da kafafen rediyo da talabijin na Najeriya NBC shiyyar Borno Ahmed Abdulkadir.

An sace Ahmed da ‘yar sa a gidan sa da ke Bakori.

Labarin ya fito ta shafin babban edita a jaridar Blueprint Ibrahim Sheme.

A yanzu dai an shiga addu’ar fatar kubutar Abdulkadir da ‘yar ta sa daga hannun barayin da ke addabar jihar Katsina.

A yanzu haka dai jami’an tsaro su na kai hare-hare a maboyar barayin a jihar Zamfara bayan kashe layukan sadarwa na waya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “AN SACE TSOHON DARAKTAN NBC NA SHIYYAR BORNO AHMED ABDULKADIR”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *