• Sun. Dec 5th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN RUFE HANYOYIN SADARWAR NA’URAR SALULA

Jihar Zamfara da wasu garuruwan kewaye sun shiga yanayin rufe layukan sadarwa na salula daga hukumar kula da kamfanonin sadarwa NCC.

Matakin ya auku ne don wasu aiyuka da jami’an tsaro za su yi a jihar kan ‘yan bimdiga da sauran masu sace mutane.

Rufe sadarwar za ta ba da damar yanke sadarwa tsakanin masu tseguntawa miyagu a daji labaru da kuma hana cinikaiyar kudin fansa da a kan yi amfani da layin wayar salula wajen gudanarwa.

Matakin ya shafi duk kafofin sadarwar yanar gizo.

Kafofin za su zama a rufe har nan da mako biyu da a ke sa ran kammala aikin jami’an a jihar ta arewa maso yamma mai tarihin kalubalen ‘yan bindiga da barayi tun bullar illar satar shanu a yankin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *