• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN MAIDA FIRAMINISTAN SUDAM HAMDOK MUKAMIN SA

ByNoblen

Nov 22, 2021

Da alamu sojoji a Sudan sun sauko da tsaurin ra’ayi biyo bayan gagarumar zanga-zanga, inda su ka dawo da firaministan kasar Abdallah Hamdok mukamin sa.

In za a tuna shugaban mulkin soja na Sudan Abdelfattah Burhan ya ture gwamnatin mika mulki ta farar hula da Hamdok ke jagoranta.
Hamdok ya fito ta kafar talabijin daga ofishin sa a fadar shugaban kasa a Khartoum don nuna ya dawo kan kujera.
An ba wa Hamdok damar kafa sabuwar gwamnati ta farar hula da za ta yi aiki da sojojin don maida kasar mulkin dimokradiyya.
Hakanan sojojin sun amince su sako fararen hular da su ka kama biyo bayan juyin mulkin da Burhan ya jagoranta.
A na sa ran gudanar da zabe a Sudan a shekara ta 2023.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.