• Tue. Oct 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN KWANTAR DA SARKI SALMAN NA SAUDIYYA A ASIBITI

An kwantar da Sarki Salman na Saudiyya a asibitin kwararru na Sarki Faisal da ke Jiddah inda a ka yi ma sa aikin duba lafiyar babban hanji.

Sarkin dai mai shekaru 86 ya shiga asibitin ranar asabar inda a ka ba shi gado.

Rahotanni na nuna aikin ya samu nasara kuma Sarkin ya samu sauki amma likitoci sun bas hi shawara ya zauna a asibtin don ya huta.

In za a tuna Sarki Salman ya kwanta kan ciwo mai kama da wannan a birnin Riyadh inda a ka yi ma sa aiki da kuma sallamar sa bayan kwanaki a shekara ta 2020.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.