• Wed. Dec 1st, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN KATSE LAYUKAN SADARWAR SALULA A WASU SASSAN KATSINA

Hukumomin Najeriya sun rufe layukan sadarwar salula a wasu yankuna na jihar Katsina inda kalubalen satar mutane ya fi ta’azzara.

Wannan ya nuna sashen Katsina ya bi sahun jihar Zamfara da hukumar kamfanonin sadarwar salula NCC ta ba da umurni a ka rufe sadarwar ta su ta salula a gaba daya jihar da ma hakan ya shafi wasu garuruwan makwabta.

Duk da dai ba wadatattun bayanan farmaki da jami’an tsaro ke kai wa kan maboyar barayi don ba sadarwa, amma bayanai daga kafafen yanar gizo na nuna jami’an tsaron na samun nasara.

Wasu masu sharhi sun yi fatar sojojin da ke kai harin za su yi amfani da duk wata dabara don tsirar da wadanda a ka sace ba tare da taba lafiyar su ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *