• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN KASHE ‘YAN SANDA A WANI HARI A JIHAR AKWA IBOM

Rahoto daga jihar Akwa Ibom a Najeriya na baiyana rasa ran jami’an ‘yan sanda biyu a sanadiyyar harin da ‘yan bindiga su ka kai mu su.

Harin ya auku ne a wani ofishin ‘yan sandan da ke karamar hukumar Ikono.

Baya ga kisan gilla ga ‘yan sandan biyu wata jami’ar ‘yan sanda ma ta samu raunuka inda a ka cinnawa motoci 5 da ke harabar ofishin wuta.

An zargi ‘yan neman raba Najeriya IPOB ne a yankin su ka kai harin kamar yanda su ke kara matsa lamba don tada fitina a yankin kudu maso kudu da kuma yankin su na asali kudu maso gabar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *