• Fri. Jan 28th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN KASHE MUTANE HAKA KURUM A YANKIN KAJURU DA KACHIA A KADUNA

Sanarwa daga gwamnatin Kaduna na baiyana cewa ‘yan bindiga sun yi kisan gilla ga mutum 8 a yankin Kajuru da Kachia.

Akasarin wadanda a ka kashe na tahowa a motar itace ne yayin da miyagun irin su ka kai mu su farmaki.

Da alamu ‘yan bindiga na takalar gwamnan Kaduna Nasir Elrufai ne don yanda ya ce ba amfanin sulhu da su gara a bude mu su wuta.

Zuwa yanzu illar na karewa kan jama’ar kauyuka da kuma ‘yan makaranta da a ke sacewa inda a yanzu haka akwai ‘yan makarantar Afaka a hannun ‘yan bindigar.

Jihar Kaduna ta zama abun tsoro wajen sacewa da kashe mutane.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *