• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN KASHE MAIGADI A OFISHIN JAKADANCIN QATAR A BIRNIN PARIS

An kashe maigadi a ofishin jakadancin Qatar da ke babban birnin kasar Faransa wato Paris amma ba a alakanta kisan da ta’addanci ba.

Duk bayanan da a ke da su zuwa rubuta wannan labari na nuna an samu asarar ran maigadi amma ba a san ko da makami a ka kashe shi ba.

Ofishin mai shigar da kara na Paris ya tabbatar da bude binciken sanadiiyyar mutuwar maigadin.

Hakanan an baiyana cewa an kama mutum daya a binciken da a ke gudanarwa na mutuwar maigadin wanda ba a baiyana sunan sa ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “AN KASHE MAIGADI A OFISHIN JAKADANCIN QATAR A BIRNIN PARIS”

Leave a Reply

Your email address will not be published.