• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN KASHE ALBARNAWI, SHUGABAN ISWAP

Labari ya zo cewa an kashe shugaban kungiyar ta’addanci ta DAESH a Afurka ta yamma ISWAP wato Albarnawy.

Majiyar jaridar Daily Trust ta tabbatar da kashe Albarnawy amma ba ta tantance yanda ya mutu ba.

Rahoton dai ya nuna wa imma sojoji ne su ka kashe shi ko kuma rashin jituwa a tsakanin ‘yan kungiyar sa ta ISWAP ta yi sanadiyyar ajalin sa.

Albarnawy dai dan marigayi shugaban Boko Haram na farko Muhammad Yusuf ne.

A tsarin Albarnawy akwai saba ka’idar kungiyar su da shugaban Boko Haram na baya Abubakar Shekau ke yi na hallaka jama’a ba tantancewa maimakon fuskantar hukuma da kokarin kafa Daula.

Albarnawy ya samu mara baya daga kungiyar DAESH ta duniya inda ya rika gudanar da hare-haren sa kan cibiyoyin jami’an tsaro da kuma a gefe guda yunkurin kawar da Shekau.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *