• Tue. Oct 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN KARA SAMUN GAWAR MUTUM BIYU DAGA GININ IKOYI DA YA RUGUJE

ByYusuf Yau

Nov 13, 2021

Zuwa yanzu an kara samun gawar mutum biyu daga benen nan mai hawa 21 da ya ruguje a Ikoyi Lagos.
Kwamishinan labarun jihar Gbenga Omotoso ya baiyana karin da nuna zuwa yanzu adadin mutum 45 a ka gano daga ginin.
A na samun sabanin alkaluman yawan mutanen da su ka mutu tsakanin gwamnatin Lagos da hukumar agajin gaggawa.
A hasashen farko dai an baiyana cewa mutum 50 ginin ya rujuge da su ciki har da mai gudanar da kwangilar Femi Osibona.
Kazalika mutum 15 a ka tabbatar sun tsira da ran su daga hatsarin.
Iyalai na zuwa da shaidar kwayar halitta don karbar gawawwakin ‘yan uwan su.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “AN KARA SAMUN GAWAR MUTUM BIYU DAGA GININ IKOYI DA YA RUGUJE”
  1. Have you ever thought about publishing an e-book or guest authoring on other blogs?
    I have a blog centered on the same subjects you discuss and would love to have you share some stories/information. I
    know my viewers would enjoy your work. If you are even remotely interested, feel free to shoot me an e mail.

Leave a Reply

Your email address will not be published.