Rahotanni daga Kano Najeriya na baiyana kammala gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar.
Jihar dai da a yanzu ke karkashin mulkin gwamnatin APC ta gwamna Abdullahi Umar Ganduje na da kananan hukumomi 44.
An ruwaito gwamnan na baiyana kyakkyawan tsari a zaben kuma da kwarin guiwar APC za ta lashe dukkan kujerun.
Ba mamaki jam’iyyare gwamna a kowacce jiha ta lashe duk kujeru don tasirin gwamnatin jiha da kuma kasancewar hukumomin zaben na karkashin jihohi ne.
Wannan lashe zabe na gaba daya ba shi da bambanci karkashin mulkin gwamnan kowacce jam’iyya musamman mafiya tasiri irin APC da PDP.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀