• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN KAMMALA AIKIN HAJJIN BANA BA TARE DA CIWO BA

An kammala aikin hajjin bana ba tare da wani cikas na rashin lafiya tsakanin alhazai dubu 60 da su ka gudanar da hajjin.

Akasarin alhazan sun fice daga Makkah bayan gudanar da dawafin bankwana.

Duk da haka wasu alhazai sun koka ga samar mu su abinci marar inganci daga kamfanonin alhazai da hakan ya sa ba su ji dadin abincin ba.

Hukumomin Saudiyya sun yi alwashin daukar matakai kan kamfanonin da su ka gaza kula da alhazan yanda ya dace.

Cikin matakan da za a dauka har da janye lasisin aikin kamfanonin marar sa bin ka’idar da a ka cimma da su.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.