• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN KAI KASHI 57% RIGAKAFIN KORONA RUKUNI NA FARKO A NAJERIYA

Zuwa yanzu Najeriya ta samu nasarar yi wa kashi 57% a rukuni na farko na gudanar da rigakafin korona bairos.

Rigakafin ya shafi wasu mutane na musamman da jami’an lafiya da za su samu karfin kariya don cigaba da aikin rigakafin har ya kai ga matakin dukkan jama’a sun samu.

Hukumar lafiya matakin farko ta Najeriya karkashin Dr.Faisal Shu’aib ke fitar da alkaluman a duk lokacin da a ka cimma wata nasara.

Kimanin allurai miliyan hudu a ka kawo Najeriya na AstraZeneca da ke karkashin wani shiri mai taken COVAX da kan tallafawa kasashe masu tasowa don samun alluran ga jama’ar su.

Akwai wadanda su ka yi korafin samun zazzabi mai zafi bayan allurar inda har zuwa bayanin nasarar nan wasu ke cewa ba za su ba da kan su a yi mu su rigakafin ba don fargabar sakamakon.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *