• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN KAI HARI KAN KWAMBAR MOTOCIN JAMI’AN SHUGABA BUHARI A KATSINA

ByNoblen

Jul 6, 2022

Miyagun iri sun kai farmaki kan kwambar motocin shugaba Buhari a jihar Katsina daidai Dutsinma.
Motocin na tafiya mahaifar shugaba Buhari wato Daura don shugaban zai zo Daura daga ketare don yin idin babbar sallah.
Mai taimakawa shugaban kan labaru Garba Shehu ya ce kwambar na dauke da jami’an tsaro, jami’an shirye-shirye da ‘yan jarida.
Shehu ya ce jami’an tsaron sun tunkari maharan inda su ka wargaza mu su shiri.
Miyagun sun makale a sassan da za su iya kwantan bauna ga tawagar.
Jami”ai biyu sun samu rauni don haka su na samun kulawar likitoci.
Fadar Aso Rock ta nuna takaicin aukuwar harin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
3 thoughts on “AN KAI HARI KAN KWAMBAR MOTOCIN JAMI’AN SHUGABA BUHARI A KATSINA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.