• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN KADDAMAR DA REDIYO ZANGON FM NA RUNDUNAR ‘YAN SANDAN NAJERIYA

ByYusuf Yau

Apr 1, 2021

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kaddamar da rediyon ta da ke kan zangon FM don yada bayanai da su ka shafi aiyukan ‘yan sanda.
Babban sufeton rundunar Muhammad Adamu ne ya kaddamar da tashar da ya ce rundunar ce ta tsara da daukar nauyin kafata.
Tashar ta FM da ke Abuja na kan mita 99.1 kuma za ta zama hanyar hada mutane da ‘yan sandan ta hanyar shiga shirye-shiryen da rediyon zai rika gabatarwa.
Sauran rundunonin tsaro kamar na soja, kwastam har ma da hukumar kiyaye aukuwar hatsura sun kafa irin wannan rediyon don yayata aiyukan su.
Ba lalle ba ne irin wadannan rediyoyin su samu masu sauraro da yawa don an san kare muradun hukumomin da su ka kafa su za su ba lalle ba da damar suka ko wata muhawara mai sarkakiya ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *