• Thu. May 19th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN KADDAMAR DA KUNGIYAR WASAN KWALLON FC ABDULKARIM DAUDA ACADEMY

Shahararren dan siyasar nan na Jahar Katsina kuma wanda mutanen jahar ke kiransa da ya tsaya takarar gwamnan jahar a zaben shekara mai zuwa 2023 watau Alh Abdulkarim Dauda ya kaddamar da Kungiyar kwallon kafa me taken FC ABDULKARIM DAUDA ACADEMY.

Dan siyasar ya kaddamar da ABDULKARIM DAUDA ACADEMY ne inda ya amsa kiran da matasan suka yi masa bayan da wani hazikin matashi Fahad Lawal ya hada kansu karkashin kulawar Malam Abubukar Yawale inda suka bujuro masa da bukatar.

Alh Abdulkarim Dauda ya saya masu dukkan abinda ‘yan kwallo suke bukata, kayan kwallon JC kala ukku ukku, kowanne kala daban-daban, har na wadanda zasu zauna a reserve acikin ‘yan wasan, kuma ya saya masu kayan training fit suma kala ukku, sannan kuma ya hada masu kwallon kafa guda goma, dadai dukkan abubuwan da team din ‘yan kwallo suke bukata.

 

Masana daga wannan bangaren kamar Dr. Shehu Ibrahim, Dr. Muhammad Lawal sun mika wadannan kayayyaki ga shugaban Kungiyar FC ABDULKARIM DAUDA ACADEMY, sannan kuma sun nunawa ‘yan wasan kwallon yadda ya kamata suyi amfani da wadannan kayayyaki a zamanance.

 

A karshe Uban tafiyar Malam Abubakar Yawale wanda ya nuna farin cikin inda ya gargadi ‘yan wasan da su kula su hada kansu, sannan shima shugaban Kungiyar Sade FIna ya nuna farin cikinsa da godiya ga Alh Abdulkarim Dauda da ya basu damar kafa wannan kungiya, haka kuma yayi godiya ga Malam Abubakar Yawale da kuma Fahad Lawal da suka tsaye masu har suka samu nasarar hakan.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “AN KADDAMAR DA KUNGIYAR WASAN KWALLON FC ABDULKARIM DAUDA ACADEMY”
  1. I have been browsing online greater than 3 hours these days, but I by no means discovered any attention-grabbing article like yours. It is lovely value enough for me. In my opinion, if all website owners and bloggers made excellent content as you probably did, the internet can be much more helpful than ever before. “Wherever they burn books, they will also, in the end, burn people.” by Heinrich Heine.

  2. I like the helpful info you provide in your articles.
    I will bookmark your blog and check again here regularly.
    I’m quite sure I’ll learn plenty of new stuff right here!
    Good luck for the next!

Leave a Reply

Your email address will not be published.