• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN KADDAMAR DA KOFIN FASSARAR ALKUR’ANI MAI GIRMA NA FARKO A HARSHEN IGBO

ByNoblen

Jul 6, 2022

A karo na farko a tarihi, an kaddamar da kofin fassarar Alkur’ani Mai Girma a harshen Igbo da Sheikh Murtala Chukwuemeka Ohajimadu ya fassara.

Taron kaddamarwar ya gudana a Masallacin ANSARUDDIN da ke anguwar Wusre 2 a Abuja.

Bayan idar da sallar jumma’a an jera kofin fassarar inda malamai su ka yi bayanin muhimmancin irin wannan aiki don samar da ilmin Alkur’ani ga jama’ar da ke amfani da harsunan su na asali don fahimtar ma’anonin cikin sauki.

“Na shafe shekaru 5 ina gudanar da wannan aiki kafin na kammala, kuma mun tura kofi 50 kasar Igbo inda mutum 24 su ka karbi Islama.” Inji Sheikh Ohajimadu.

Shehun malamin ya kara da cewa akwai fassarar Alkur’ani a harshen Hausa na Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da wani da a ka yi a harshen yarbanci, wanda hakan ya ba shi kwarin guiwar gudanar da aikin fassarar don al’ummar Igbo su amfana.

Alhaji Shahru Umar ne ya jagoranci taron kaddamarwar ya na mai cewa aiki ne mai mhuimmanci da su ka sanyawa hannu don samun kammala shi.

Hakimin Galadimawa a Abuja Alhaji Musa Barde ya bukaci sauran masu hannu da shuni su tallafa don samar da kofin fassarar mai yawa don a cigaba da rabawa jama’a.

Mutane sun yi dafifi su na bude kofin su na dubawa duk da akasrin su ba sa fahimtar harshen Igbo in ka debe NSO da a ka ce na nufin mai tsarki wato NSO ALKUR’AN, Sai CHUKWU-Allah mai girma.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.