• Sun. Nov 28th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN KADDAMAR DA HARE-HAREN JIRGIN SAMA KAN ‘YAN TAWAYEN HOUTH DON SAMUN KAI KAYAN AGAJI

ByHassan Goma

Oct 13, 2021 ,

 

Rahotanni daga Yaman na baiyana cewa an kaddamar da hare-hare ta sama kan ‘yan tawayen houthi da Iran ke marawa baya don samun isa sassan da su ka tare da kan hana kai kayan agaji.

Mutum dubu 35 ne ke cikin bukatar tallafi amma hakan ya gagara don fitinar da ke daukar dogon lokaci don gwagwarmayar kwace yankin Marib mai arzikin iskar.

Rundunar Larabawa da Saudiyya ke jagoranta ta kaddamar da harin kan Al-Abedia da ke yankin Marib inda ‘yan tawayen su ka kule tsawon kwana 20.

Rundunar ta ce ta kai hare-hare 43 a tsawon sa’a 24 kan mayakan houthi inda ta hallaka 134 da lalata motocin yaki 9

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “AN KADDAMAR DA HARE-HAREN JIRGIN SAMA KAN ‘YAN TAWAYEN HOUTH DON SAMUN KAI KAYAN AGAJI”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *