• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN KADA KURI’AR RASHIN GAMSUWA DA GWAMNATIN BUHARI INDA A KA GWALE SANATA DANSADAU

An kada kuri’ar dawowa daga rakiyar gwamnatin Buhari yayin da mutane kuma su ka gwale Sanata Sa’idu Dansadau da ya yi wuf ya amshe bututun magana daga Imam Ibrahim Auwal Usama.

Wannan lamari ya auku a lokacin jawaban sallar idin karamar sallah a masallacin anguwar ‘yan majalisar dokokin Najeriya da ke Apo Abuja.

Masallacin dai wanda tun a tarihi jama’a su ka tara kudi su ka gina ya na daf da gidan nan na kakakin majalisar wakilai da gyaran gidan kan Kimanin Naira miliyan 600 ya haddasa tsige kakakin majalisa Patricia Eteh har Allah ya karbi rayuwar dan majalisa Shu’aibu Safana.

Lokacin da Imam Ibrahim Auwal Usama ke jawabi ya nuna rashin tabuka abun kirki na gwamnatin Buhari ga al’ummar arewa da karfafa cewa tamkar ‘yan kudu ne su ke cin gajiyar gwamnatin alhali shugaban dan tsakiyar arewa ne.

Imam Usama ya ba da misali da rashin kammala gyaran hanyar Abuja zuwa Kano da tabarbarewar tsaro.

Wannan ya sa dan siyasar jihar Zamfara tsohon Sanata Sa’idu Dansadau ya kasa jurewa ya zo ya karbe na’urar magana ya ce a yi wa gwamnatin shugaba Buhari adalci don ta ba da tallafi ko basuka ga jama’a.

Hakan ya sa mutane fusata da bukatar ya rufa mu su baki, inda shi kuma ya ce irin wannan bijirewa hatta Annabawa an yi mu su irin ta.

Dansadau wanda duk da dan siyasa ne kan karantar da littafin AHLARI a karamin masallacin jumma’a na anguwar da ke Zone A.

Imam Usama ya karbi abun magana inda ya jagoranci kada kuri’ar dawowa daga rakiyar gwamnatin shugaba Buhari.

Anguwar Apo dai ta kasance da tsoffin ‘yan majalisa da sabbi da kuma masu hannu da shuni tun sanadiyyar neman tazarcen shugaba Obasanjo gabanin zaben 2007 ya sayarwa ‘yan majalisa gidajen tamkar kyauta don neman a mara ma sa baya. Lokacin Nasiru Elrufai ke ministan Abuja.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.