• Sun. Nov 28th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN JUYA KALAMAN SHUGABA BUHARI BAIBAI A ZIYARAR SA TA IMO-ADESHINA

Kakakin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, wato Femi Adeshina ya ce wasu masu son juya bayani sun birkita ma’anar wani furuci na shugaba Buhari a gidan gwamnatin Imo a ziyarar aiki da ya kai jihar a makwan jiya.

Shugaban dai bisa gaiyatar gwamna Hope Usodinma, ya kammala jawabin sa da cewa “zan yi takatsantsan da gaiyatar ka nan gaba.”

Masu yada har faifan bidiyo daidai kalaman na fassarawa da cewa shugaba Buhari ya gwale gwamna Uzodinma ne don bai ji dadin ziyarar ta Imo ba inda nan ne tamkar helkwatar zubar da jini don kafa kasar Biyafara.

Adeshina ya ce abun da shugaban ke nufi shi ne jin dadin sa don ya dauka aiyuka kadai zai kaddamar sa ya ga Uzodinma ya tara ma sa manyan ‘yan yankin jihohin Igbo 5 su 50 don tarbar sa a Owerri.

Adeshina ya ce ganin manyan mutanen ya sa shugaban nuna nan gaba zai san yanda zai yi in Uzodinma ya sake gaiyatar sa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *