‘Yan ta’addan da a ke ganin ISWAP ne sun sace fasinjoji 15 a kan hanyar Chibok zuwa Damboa su ka shige da su dajin Sambisa.
An gano wadanda a ka sacen jami’an kungoyin agaji ne da ke kan hanyar su ta zuwa Yola jihar Adamawa don halartar wani taro.
Hanyar dai da ta zama mai hatsari, ba ta fi tsawon kilomita 45 ne kuma a yanzu haka a na kan aikin shunfuda ta.
Gabanin nan ma ‘yan ISWAP din sun ce ma’aikatan ma’aikatar aiyuka na jihar ta Borno sun shirya tafiya da motoci 4 ciki da Hilux.
Sharhi kan labarin na nuna ‘yan ISWAP din na son samun karin mutane ne da za su shigar da su ta’addanci.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀