• Tue. Oct 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN HALLAKA ‘YAN TAWAYEN HOUTHI NA YAMAN 48 A DAF DA BIRNIN MARIB

ByHassan Goma

Oct 20, 2021 , ,

 

Rundunar hadin guiwar larabawa da Saudiyya ke jagoranta don tallafawa Yaman, ta ce ta hallaka ‘yan tawayen houthi 48 a daf da birnin Marib.

A hare-hare 14 cikin sa’o’I 24, rundunar ta baiyana hallaka ‘yan tawayen da kuma lalata motocin yakin su 6.

Harin murkushe ‘yan tawayen ya auku ne a garin Alkassara da Al-Jawba.

Rundunar ta ce za ta cigaba da karfafa rundunar sojan yaman don kare lafiyar al’ummar kasar daga mamayar ‘yan tawayen.

Marib dai yanki ne mai arzikin iskar gas da ya zama shi kadai ya rage a hannun gwamnatin kasar a arewaci.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
13 thoughts on “AN HALLAKA ‘YAN TAWAYEN HOUTHI NA YAMAN 48 A DAF DA BIRNIN MARIB”
  1. I am extremely impressed with your writing skills and also
    with the layout on your blog. Is this a paid theme
    or did you modify it yourself? Anyway keep up the nice
    quality writing, it’s rare to see a nice blog like this one these days.

  2. I read this article fully regarding the comparison of
    most recent and previous technologies, it’s amazing article.

Leave a Reply

Your email address will not be published.