• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN HALLAKA MAI HADA BOM NA ‘YAN TAWAYEN HOUTHI A YANKIN HAJJAH

ByNoblen

Mar 11, 2022

An hallaka mai hada boma-bomai na kungiyar ‘yan tawayen houthi da Iran ke marawa baya a Yaman, a yankin Hajjah na arewacin.
Mai hada bom din Abdul’aziz Ahmed Al-Abed dai injiniyan na’urori ne wanda a ke zaiyanawa daga cikin ‘yan tawayen mafiya hatsari.
Mataimakin gwamnan yankin Nasseer Dagin ya ce Al-Abed wanda a ka haifa a yankin, ya hada boma-bomai da nakiyoyi da su ka yi sanadiyyar rasa ran dubban ‘yan Yaman.
‘Yan houthi sun baiyana cewa Al-Abed ya shiga yaki a sassa daban-daban don kare muradun houthin, kuma ya na daya daga mayakan da su ka kai harin kwace babban birnin kasar San’a’a a 2014.
‘Yan tawayen sun bunne nakiyoyi da su ka kai miliayn 1 musamman a yankunan da a ke yaki da su ka hada da Jouf, Shabwa, Sa’ada Hodeida da Marib.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “AN HALLAKA MAI HADA BOM NA ‘YAN TAWAYEN HOUTHI A YANKIN HAJJAH”
  1. I always used to read post in news papers but now as I
    am a user of internet so from now I am using net for articles or reviews,
    thanks to web.

Leave a Reply

Your email address will not be published.