• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN GUDANAR DA ZABEN SHUGABAN KASA A GAMBIA INDA A KA SHIGA KIDAYAR KURI’A

ByNoblen

Dec 5, 2021

Tuni an fara kidayar kuri’a a zaben shugaban kasar Gambia da ya gudana karo na farko tun takaddamar zaben da shugaban da ke kan gado Adama Barrow ya samu da tsohon shugaban kasar Yahaya Jammeh.
Zaben na da tsari na daban da sauran kashe inda maimakon kada kuri’a da takarda, a kan jefa kamar ‘yan duwatsu ne cikin akwatin dan takara daga nan in an kammala sai a shiga kidayawa.
Za a iya cewa an yi kan-kan-kan a tsarin zaben da shugaba Barrow ke fuskantar mafi girman kaluble daga tsohon maigidan sa Ousainou Darboe mai shekaru 76.
Barrow mai shekaru 56 ya kada kuri’ar sa a birnin Banjul da rakiyar matan sa biyu ya na mai nuna kwarin guiwar lashe zaben.
A na sa ran fitowar sakamakon zaben a lahadin nan.
 

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *