An gudanar da zaben kananan hukumomi a babban birnin Najeriya Abuja inda a ka samu karancin fitowar masu kada kuri’a.
Zaben dai na kananan hukumomi 6 na Abuja, shi kadai ne hukumar zaben taraiya INEC ke gudanarwa da kan ta a dukkan zaben kananan hukumomi 774 na Najeriya.
Wasu daga masu kada kuri’a sun koka kan yanda na’urar masu kada kuri’a ta rika samun tangarda a lokacin tantance jama’a.
Masu sharhi na cewa akwai bukatar kara shawo kan jama’a don su rika fitowa zabe da hakan zai sa babban zaben 2023 ya yi nasara.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
I was searching everywhere a post like that.
I was searching everywhere a blog post like this for quite a long time.