• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN GUDANAR DA JANA’IZAR WADANDA SU KA RASA RAN SU A HARE-HAREN ‘YAN BINDIGA A KAUYUKAN ANKA

Rahotanni daga masu gudun hijira a garin Anka da ke jihar Zamfara sun baiyana cewa an gudanar jana’izar wadanda su ka rasa ran su a sanadiyyar harin ‘yan bindiga a kauyukan yankin na Anka.
An ba da labarin tattaro wasu gawawwaki daga dazuka da yi mu su sutura a manyan ramuka.
Ynazu haka ‘yan gudun hijira na nan a cikin gari a Anka sun a samun mafaka a makarantun firamre da neman taimako daga jama’ar gari.
Wani jami’in gwamnati ya baiyana cewa an samu matsalar yayin da ‘yan bindiga ke kauracewa yankunan jihar Sokoto su na shiga Zamfara don farmaki da jami’an tsaro ke kai mu su.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *