• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

AN GUDANAR DA JANA’IZAR DR.IBRAHIM DATTI AHMED A MASALLACIN ALFURQAN KANO

ByNoblen

Dec 31, 2021 ,

An gudanar da sallar jana’izar shugaban majalisar shari’ar musulunci ta Najeriya Dr.Ibrahim Datti Ahmed a masallacin Alfurqan da ke Kano.
Marigayin ya rasu bayan fama da jinya ya na mai shekaru 83.
Dr.Datti Ahmed wanda likita ne kuma jagoran addini, shi ya fara bude asibiti mai zaman kan sa don tallafawa gwamnati wajen lamuran kiwon lafiya.
Rahoto ya nuna marigayin ya samu kimanin shekaru biyu ya na fama da jinya kafin a ‘yan kwanakin nan ciwon ajalin ya zo da ya shafi ciwon suga.
Sunan marigayin ya kara fitowa a duniya ne lokacin gwagwarmayar samun shari’a a wasu jihohin arewa don cusa amana da da’a a zukatan al’umma.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *